CAF: Toure da Mikel da Drogba suna takara

Image caption Yaya Toure da Mikel Obi da kuma Didier Drogba

Dan kwallon Ivory Coast da Manchester City, Yaya Toure na kan hanyarsa ta zama gwarzon dan kwallon Afrika a karo na uku a jere.

Hukumar dake kula da kwallon Afrika wato CAF ta kebe sunayen 'yan kwallo uku don bada kyautar zakaran kwallon nahiyar na 2013.

Baya ga Yaya Toure akwai sunan John Mikel Obi na Chelsea da Nigeria da kuma dan Ivory Coast Didier Drogba.

Yaya Toure mai shekarun haihuwa 30, shine ya samu kyautar a shekara ta 2011 da kuma 2012.

Wannan ne karon farko da Mikel Obi na Chelsea mai shekaru 26 ya shiga cikin jerin.

Didier Drogba mai shekaru 35 wanda ke taka leda a Turkiya tare da Galatasaray ya samu kyautar a shekara ta 2006 da kuma 2009.

A ranar 9 ga watan Junairu za a sanar da gwarzon dan kwallon Afrika na 2013 a wani buki da za a yi a Lagos.

Karin bayani