Paulinho zai yi jinyar wata daya

Image caption Paulinho

Dan wasan Tottenham Paulinho zai yi jinyar akalla wata guda sakamakon rauni a idon sawunsa lokacin da ya yi karo da dan wasan Stoke, Charlie Adam.

Paulinho mai shekaru 25, za a buga wasanni hudu banda shi a gasar Premier.

Dan kwallon na kasar Brazil a watan Yuli ya hade da Spurs daga Corinthians a kan kusan fan miliyan 17.

Charlie Adam an kwana biyu ana cece kuce a kan yadda yake kaiwa 'yan kwallo hari saboda a baya ya taba turguda Gareth Bale.

Karin bayani