Schumacher na samun sauki

Image caption Zakaran gasar Formula one, Micheal Schumacher

Likitocin dake kula da tsohon zakaran tseren motoci na duniya, Michael Schumacher sun ce sun kara yi masa tiyata a karo na biyu a cikin dare a kwakwalwarsa, kuma yana samun sauki.

Likitocin a wani asibiti dake Grenoble sun ce Schumacher ya dan farfado amma kuma har yanzu yana cikin hadari.

An yi masa tiyatar a daidai lokacin da iyalansa sun kwana a gefen gadonsa suna masa addu'o'i.

Schumachar ya samu buguwa ne a kansa lokacin wani hadari wajen zamiyar kankara, a yankin tsaunukan Faransa, French Alps a ranar Lahadi, inda ya shiga yanayi na rai kwakwai mutu kwakwai.

Karin bayani