Kamaru za ta kara da Portugal

Cameroon Portugal
Image caption Kamaru na fatan taka rawar gani a gasar kofin duniya

Kamaru ta cimma yarjejeniyar karawa a wasan sada zumunci da Portugal da Argentina, a kokarin ganin ta tabuka rawar gani a gasar kofin duniya da za a buga a Brazil.

Dukkansu kasashen sun samu gurbin shiga gasar kofin duniya a Brazil da za a fara fafatawa daga ranar 12 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli.

Kamaru za ta fara karawa da Portugal a wasan sada zumunci ranar 6 ga watan Maris, sannan ta barje gumi da Argentina ranar 6 ga watan Yuni.

Haka kuma tawagar The Indomitable Lions za ta fafata da Jamus ranar 1 ga watan Yuni, duk dai a kokarin ganin ta taka rawar gani a kofin duniya.

Kasar da ke da koci Volker Finke, na da jan aiki ganin an hada ta rukuni daya da Brazil, Mexico da Croatia.