Solskjaer ya zama kocin Cardiff City

Ole Gunnar Solskjaer
Image caption Cardiff City tana matsayi na 17 a teburin Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City ta nada Ole Gunnar Solskjaer a matsayin sabon kocinta.

Tsohon dan kwallon Manchester United din, mai shekaru 40, ya halarci filin atisayen kungiyar a dazu, kafin Kulob din ya sanar da daukar kocin a katafaren filin wasansa ga 'yan jaridu.

Kafin zuwansa Cardiff, Solskjaer, ya horar da Molde FK da ke Norway, kuma ya maye gurbin Malky Mackay da kungiyar ta kora.

Sabon kocin ya ce "Kalubale ne mai girma a tare da ni, kuma Cardiff a shirye take na ganin ta kai gaci, da fatan zan ba da gudunmawa".