Heitinga ya ki ya koma West Ham

Johnny Heitinga
Image caption Dan wasan bai samu bugawa Everton wasa a bana ba

Dan kwallon Everton Johnny Heitinga ya ki amincewa ya koma West Ham duk da kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniyar sayen dan wasan.

Dan wasan mai tsaron baya mai shekaru 30, ya ce "Maganar ba akan kudi bane domin West Ham bata da matsalar kudi, ina da tabbacin zan samu wata kungiyar na koma wasa kafin karshen watan Janairu."

West Ham na kokarin daukar dan wasan da zai maye gurbin James Tomkins da James Collins da suke jinyar rauni, Tuni kocin West Ham Sam Allardyce da a baya ya bada sanarwar cimma yarjejeniyar daukar Heitinga, yanzu ya ce za su sake neman wani dan wasan.

Heitinga wanda ya koma Everton daga Atletico Madrid kan kudi kimanin fam miliyon 7 a shekarar 2009, baya bugawa Holland wasanni sakamakwon rashin bugawa Everton wasa a kakar bana.