Laudrup: Swansea za ta kara kaimi

 Michael Laudrup
Image caption Swansea za ta sa kaimi domin ci gaba da buga gasar Premier ta badi

Kocin Swansea City, Michael Laudrup, ya ce kungiyarsa za ta kara kaimi matuka na ganin ba ta fado daga tebirin gasar Premier a bana ba.

Kungiyar ta samu maki uku daga cikin wasanni shida da ta buga a baya, kuma tana matsayi na 13 a teburin.

Swansea ta yi rashin nasara a hannun Manchester City har gida da ci 3-2 a karawar da suka yi ranar Laraba, kuma za ta fafata da Manchester United da Tottenham Hotspur a wasannita biyu masu zuwa.

Kocin ya ce, "Matukar 'yan wasanmu za su kara kaimi a wasannimu na gaba ina da tabbacin za mu ci gaba da zama daram a gasar Premier ta badi."

Rabon Swansea ta samu nasara a wasa, tun lokacin da ta casa Newcastle da ci 3-0 a farkon watan Disamba.