Ba zan sayi dan kwallon gaba ba- Mourinho

Image caption Jose Mourinho

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce tabbas ba zai sayi wani sabon dan wasan gaba ba a kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Junairu.

Chelsea nada 'yan wasa uku na gaba wato Fernando Torres, Demba Ba da kuma Samuel Eto'o amma a tsakaninsu sun zura kwallaye bakwai ne a gasar Premier ta bana, abinda yasa ake ganin cewar kungiyar na bukatar sabon dan kwallo mai zura kwallo.

Mourinho ya ce " Tabbas ba zamu saye wani dan kwallo ba".

Tsohon dan kwallon Chelsea Jimmy Floyd Hasselbaink, dai ya ce kungiyar na bukatar sabon dan wasan gaba don ta ci gaba zura kwallaye.

Karin bayani