Eusebio dan kwallon Portugal ya rasu

Eusebio da Silva Ferreira
Image caption Dan wasan ya yi fice wajen zura kwallo a raga

Fitaccen dan kwallon Portugal Eusebio, wanda yafi kowa yawan zura kwallo a gasar kofin duniya a shekarar 1966, ya rasu bisa ciwon juciya, yana da shekaru 71.

Dan wasan wanda aka haifa a Mozambique a shekarar 1942, lokacin kasar na karkashin mulkin mallakar Potugal, ya samu damar bugawa Portugal wasanni 64 ya kuma zura kwallaye 41.

Eusebio da Silva Ferreira dan wasan Benfica ta Portugal, ya zura kwallaye tara a gasar kofin duniya da Ingila ta karbi bakunci a shekarar 1996, ciki har da kwallaye hudu da ya zura a ragar Korea ta Arewa.

Dan wasan da ya yi fice a zamaninsa, ya zura kwallaye 733 daga cikin wasanni 745 da ya buga a kwararren dan wasa.

Dan kwallon ya sha fama da jinyar ciwon zuciya da toshewar kafar jini da aka dinga kai shi asibiti sau da dama a baya.