Chelsea ta doke Coventry da ci 2-0

Kungiyar Chelsea ta samu kaiwa wasan zagaye na hudu, bayan da ta doke Coventry City da ci 2-0 a gasar kofin kalu-bale wasan zagaye na uku.
Image caption Chelsea za ta kara da Stoke City a wasan zagaye na hudu a kofin FA

Kungiyar Chelsea ta samu kaiwa wasan zagaye na hudu, bayan da ta doke Coventry City da ci 2-0 a gasar kofin kalu-bale wasan zagaye na uku.

John Mikel Obi da Oscar sune suka zura kwallayen biyu a raga, da ya baiwa Chelsea damar kaiwa wasan zagaye na hudu da zata karbi bakuncin Stoke City a Stamford Bridge.

Mikel ne ya fara zura kwallon farko da kai lokacin da Willian ya bugo kwallo, daga baya Oscar ya zura kwallo ta biyu a raga, a kwallon da ya buga mai zafi ta kuma fada raga.

Ramires ma ya kusan zura kwallo a raga, sai kwallon ta doki turke, kwallo daya kacal Derby ta kai harin da ya girgiza golan Chelsea Mark Schwarzer lokacin da dan wasanta Chris Martin ya buga masa kwallo .

Sai dai an baiwa Ramires katin gargadi lokacin da ya fadi a da'ira ta 18 a karo na biyu da gangan.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya amince da aka baiwa Oscar katin gargadi a faduwar da yayi da gangan a karawar da suka lashe Southampton da ci 3-0 a ranar Laraba a gasar kofin Premier.