Lewandowski zai koma Bayern Munich

Robert Lewandowski
Image caption A karshen kakar bana kwantaraginsa za ta kare da Dortmund

Robert Lewandowski ya rattaba hannu zai koma Bayern Munich, a lokacin da kwangilarsa ta kare da Borussia Dortmund a karshen kakar bana cikin watan Yuni.

Dan wasan mai shekaru 25, dan kwallon Poland ya amince da kwangilar shekaru biyar da Bayern Munich,

Lewandowski ya zura kwallaye 16 jumulla a kungiyarsa da kasarsa a kakar bana, har da kwallon da ya zurawa Arsenal a gasar cin kofin zakarun Turai da Dortmund ta lashe wasa da ci 2-1 a watan Oktoba.

Dan wasan ya zama fitaccen dan kwallon Dortmund na biyu da ya bada sanarwa zai koma Bayern Munich, bayanda Morio Gotze ya koma filin wasa na Allianz Arena kan kudi fan miliyan 31 a watan Afirilun bara.