Omeruo zai koma Middlesbrough

Kenneth Omeruo
Image caption Dan wasan yana son bugawa Nijeriya kofin duniya a bana

Dan kwallon Nijeriya mai tsaron baya Kenneth Omeruo, zai koma kungiyar Middlesbrough daga Chelsea a aro ranar Litinin din nan.

Kocin Middlesbrough Aitor Karanka ya tabbatar da daukar dan wasan, bayan da kungiyarsa ta sha kashi a hannun Hull da ci 2-0 a kofin Kalu-bale wasan zagaye na uku.

Dan wasan mai shekaru 20, yana atisaye da manyan 'yan wasan Chelsea, amma baya samun damar buga wasa, sannan yana hankoron bugawa Nigeriya gasar kofin duniya a bana, shi yasa ya amince ya koma Middlesbrough wasa.

Omeruo ya koma Chelsea daga kungiyar Standard Liege a watan Janairun 2012, kuma nan take kungiyar ta bada shi aro zuwa kungiyar ADO Den Haag dake Holland.

Tun daga lokacin dan wasan ya sa kwazo har Nijeriya ta gayyato shi gasar kofin nahiyar Afirka, ya kuma bugawa Nijeriya wasa har ta lashe kofin Afirka a shekarar 2013.