Gareth Bale ya samu saukin rauni

Gareth Bale
Image caption Dan kwallon yana fama da jinyar rauni a Madrid

Gareth Bale ya sami saukin raunin da ya ji a kafarsa, harma Real Madrid ta saka sunansa a cikin tawagar 'yan wasan da za su kara da Celta Vigo a yau Litinin a gasar Laliga wasan sati na 18.

Dan wasan dan kwallon Wales ya ji raunin ne a lokacin da suke atisaye kafin Kirsimeti, dalilin da yasa bai samu buga karawar da kungiyar tayi da Olimpic Xatvia a kofin Copa del Rey da kuma wasan da Madrid ta doke Valencia da ci 3-2 a watan jiya.

Bale, mai shekaru 24, ya komo atisaye ne a cikin wannan satin, kuma koci Carlo Ancelotti ya ce "Zai saka dan wasan a karawar da kungiyar za tayi da Celta Vigo."

Dan wasan Tottenham da yayi fice a shekarar bara wanda Real ta saya a kan kudi fan miliyan 85, ya zura kwallaye biyar a wasanni biyar da ya bugawa Real Madrid.

Real Madrid tana matsayi na uku a teburin La Liga, wacce Barcelona dake matsayi na daya ta bata tazarar maki takwas,