Da wuya Man U ta dau 'yan wasa

Image caption David Moyes na fuskantar kalubale bayan da Manchester United ta sha kaye a gida sau hudu a wasanni shida.

Kocin Manchester United David Moyes ya ce zai yi wuya ya karfafa kungiyarsa cikin Janairu saboda babu wadatar kwararrun 'yan wasa da zai iya dauka a watan.

Ya ce: "Muna bukatar kawo sababbin 'yan wasa amma mafi yawan wadanda muke nema ba zasu samu ba a Janairu."

Marouane Fellaini, wanda dan wasan Moyes ne a tsohuwar kungiyarsa ta Everton, ne kadai sabon dan wasan da United ta dauka a karshen kakar bara.

Kungiyar mai rike da kambun Premier, wacce take ta bakwai a rukunin a yanzu, ta sha kaye hannun Swansea a Old Trafford inda ta fitar da ita daga kasar kofin kalubale.