An caka wa dan Oldham wuka a Liverpool

Image caption Liverpool ta doke Oldham 2-0 a gasar kofin kalubale.

An caka wa wani magoyin bayan Oldham Athletic wuka bayan da kungiyarsa ta buga wasa da Liverpool a gasar cin kofin kalubale ranar Lahadi.

Jami'an 'yan sanda na Merseyside sun ce mutumin mai shekaru 35 ya tare wata motar daukar mara sa lafiya ne a yankin Anfield jim kadan bayan wata hatsaniya da misalin karfe biyar agogon GMT.

Kakakin 'yan sandan ya ce mutumin, wanda rauninsa bai kai gargara ba, ya ki bai wa masu bincike karin bayani.

'Yan sandan sun bukaci sauran 'yan kallon wasan da masu motocin da suka wuce ta hanyar da su taimaka da karin bayani. Liverpool ce ta yi nasara a wasan 2-0.