Walcott zai yi jinyar watanni shida

Theo Walcott
Image caption Dan wasan ya yi fama da jinyar rauni a kakar bana

Dan wasan Arsenal Theo Walcott ba zai bugawa Ingila gasar kofin duniya ba, sakamakon zai yi jinyar rauni na tsawon watanni shida da yaji a gwiwarsa.

Dan kwallon Ingila mai wasan gaba mai shekaru 24, ya ji raunin ne a lokacin da Arsenal ta lashe Tottenham da ci 2-0 a kofin kalu-bale da suka kara a ranar Asabar.

Arsenal ta bada sanarwar ce wa "Theo ya gamu da tsagewar tsoka da gocewar kashi a gwiwarsa.

"Za a yiwa dan wasan tiyata nan ba da daewa ba, kuma zai yi jinyar watanni shida, ba zai dawo kwallo ba har sai bayan kakar wasan bana, ba zai kuma bugawa Ingila gasar kofin duniya ba."