Masu West Ham sun goyi bayan Allardyce

Image caption West Ham ta yi nasara daya cikin wasanni 13 a Premier.

Mutane biyun da suka mallaki kungiyar West Ham, David Gold da David Sullivan sun bayyana goyon bayansu ga koci Sam Allardyce.

Kungiyar ta sha kayen 5-0 hannun Nottingham Forest mai buga wasa a rukunin Championship a gasar cin kofin kalubale ranar Lahadi.

West Ham dai ita ce ta biyun karshe a teburin Premier bayan da ta samu nasara daya tal cikin wasanni 13.

Allardyce, mai shekaru 59, ya zuba matasa ne a wasan Forest bayan da ya yi sauyi tara ga 'yan wasan da suka sha kaye a karonsu da Fulham a rukunin Premier.

Kocin Hammers din ya ce ya bada muhimmanci ne ga wasannin kungiyar a Premier tare da karon wasan daf da na karshe a gasar cin kofin Capital One da za ta buga da Manchester City kuma ya sanar da Gold da Sullivan game da shirinsa.