Messi zai bugawa Barcelona wasa

Lionel Messi
Image caption Messi zai buga wasa a Copa del Rey a Nou Camp

Lionel Messi zai dawo buga wa Barcelona kwallo a karawar da kungiyar za ta yi da Getafe a gasar Copa del Rey ranar Laraba, bayan da ya samu saukin raunin da ya ji.

Dan wasan mai shekaru 26, yayi fama da jinyar raunin da ya ji tun a 10 ga Nuwamban bara, amma zai dawo buga wasan da za su karbi bakuncin Getafe a Nou Camp.

Dawowar Messi wasa ta zo daidai lokacin da kungiyar za ta kara wasa mai zafi da Atletico Madrid ranar Asabar a gasar La liga wasan mako na 19.

Barcelona na matsayi na daya a teburin La liga da maki 40 dai dai da Atletico amma da tazarar kwallaye a raga, bayan karawa a wasannin 18.

Messi ya yi fama da jinyar rauni a bara, na baya bayan nan shi ne wanda ya ji a karawar da suka lashe Real Betis da ci 4-1.