Aguero zai dawo kwallo a wannan watan

Sergio Aguero
Image caption Idan ya dawo wasa zai karawa kungiyar kaimi

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce Sergio Aguero na daf da dawo wa kwallo a cikin Janairun nan, bayan jinyar rauni da ya yi fama da shi.

Dan wasan mai shekaru 25, rabonsa da wasa tun ranar 14 ga watan Disambar bara a karawar da suka yi da Arsenal, wanda an za ci zai yi jinyar watanni takwas.

Aguero ya zura kwallaye 19 a wasanni 20 da ya bugawa City a kakar wasan bana, kuma idan ya dawo wasa zai karawa kungiyar karfin gwiwa a kokarin da taka na taka rawar gani a kakar wasan bana.

City za ta kara da Tottenham da Chelsea a gasar Premier a wannan watan, sannan ta karbi bakuncin Barcelona a karawar da za suyi a gasar kofin zakarun Turai a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.