Ronaldo ya ci kwallo ta 400

Image caption Ana sa ran Ronaldo ne zai lashe Ballon d'Or

Cristiano Ronaldo ya zura kwallonsa ta 400 a wasan da Real Madrid ta casa Celta Vigo tare da tsuke gibin dake tsakaninta da jagorar La Liga, Barcelona.

Kwallaye biyun da Ronaldo ya ci a wasan, wadanda su ka mai da shi na hudu a yawan kwallaye a tarihin Real Madrid a gasar La Liga, sun ceco kungiyar da ke matsayi na uku a bayan Barcelona da Atletico Madrid.

Yanzu haka kyaftin din Portugal ya zura kwallaye 400 a wasanni 653 a tsawon rayuwarsa - adadin kwallayen da ya ci a bana sun kama 28 ke nan.

Wannan makon zai iya zama na tarihi ga dan wasan gaban na Real kasancewar ranar 13 ga Janairu ne za'a bayyana wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or wacce ake sa ran zai yi nasara.