Carroll yana dab da dawo wa kwallo

Andy Carroll
Image caption Dan wasan ya yi fama da jinyar rauni da ya ji a kafarsa

Kocin West Ham Sam Allardyce ya ce dan kwallon da kungiyar ta saya mafi tsada Andy Carroll ya kusa ya dawo kwallo, bayan da ya sha fama da jinya.

Caroll -- dan shekaru 25 -- da kungiyar ta saya daga Liverpool bai samu damar buga wasa ba sakamakon raunin da ya ji a kafarsa.

Allardyce ya ce, "Andy ya yi atisaye da 'yan wasa a yau, muna fata zai zauna a benci nan da sati mai zuwa.

"Idan Carroll ya dawo atisaye zai kara mana karfin gwiwa, kungiyar da take matsayi na biyun karshe a teburin Premier."

Dan wasan dan kwallon Ingila ya zura kwallaye bakwai a wasanni 24 da ya bugawa Hammers a kakar wasan bara, sanda yaje kungiyar aro daga Liverpool.