Rodgers ya yarda da tuhumar FA

Brenden Rodgers
Image caption Kocin zai saurari hukuncin da FA za ta dauka a kansa

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya amince da tuhumar da hukumar kwallon kafar Ingila ta yi masa bisa kalaman da ya yi, bayan da kungiyarsa ta sha kashi a hannun Manchester City.

Rodgers ya zargi yadda alkalin wasa daga Bolton Lee Mason, ya gudanar da aikinsa bayan da aka tashi wasan da aka doke su da ci 2-1.

Kocin a lokacin ya ce "Ina fatan za mu samu kwararren alkalin wasa a karawar da za mu sake tsakani Liverpool da Manchester City a nan gaba."

Hukumar FA za ta ladabtar da shi a dan gajeren zama da za ta yi ba tare da kocin ya halarci zaman ba.

Rodgers, mai shekaru 40, ya fayyace tun a baya bisa zargin da ya yi ranar 26 ga watan Disamba cewar bai tuhumi kwarewar alkali Mason a karawar da suka yi ba.