Kasashe 51 sun yi rijistar gasar kofin Afirka

Chan Qualifier 2014
Image caption Morocco ce za ta karbi bakuncin gasar 2015

Kasashe 51 ne dai suka yi rigistar wasannin neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za a fafata a shekara ta 2015.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta ce kasashe biyu ne daga cikin 54 da suka hada da Somalia da Djibouti da su ka ki shiga wasan neman cancantar shiga kofin Nahiyar Afirka.

Tuni mai masaukin baki Morocco ta sami tikitin buga gasar da za a fafata a shekarar bara tun daga ranar 15 ga watan Janaitu zuwa 15 ga watan Fabrairu.

CAF za ta zauna ranar 24 ga watan Janairun nan a Cape Town ta Afrika ta Kudu domin tantance salon da za a bi a wasannin neman tikitin gasar.

Tun a farko an dage fitar da jaddawalin wasannin ne da aka shirya gudanarwa ranar 31 da watan Janairu aka maida shi watan Afrilun bana, lokaci daya da za a fidda jaddawalin gasar kofin zakarun Nahiyar Afirka wato African Champions League da Confederation Cup.

Za a fafata a wasannin neman tikitin kofin Nahiyar Afirka ne a tsawon watanni uku da za a fara buga wasannin share fage sannan a buga wasannin rukunnai da zarar an kammala gasar kofin duniya a bana.