Hitzlsperger ya ce shi dan luwadi ne

Thomas Hitzlsperger
Image caption Dan wasan farko da ya bayyana kansa a Ingila yana luwadi

Tsohon dan kwallo Aston Villa, Thomas Hitzlsperger, ya ce shi dan luwadi ne.

Hitzlsperger, mai shekaru 31, ya bugawa Jamus wasanni 52 kuma ya ba da sanarwar halayyarsa ta luwadi a mujallar Die Zeit.

Tsohon dan kwallon na West Ham da Everton, shi ne fitaccen dan kwallo da ya fito fili ya sanar cewa shi dan luwadi ne, yana mai karawa da cewa "lokaci ne ya yi da na sanarwa duniya matsayina."

Haka kuma ya ce, "Ya sanarwa da duniya halayyarsa ne domin a tattauna a kuma ciyar da harkar luwadi gaba a tsakanin 'yan wasa da jama'a''.

Dan wasan ya ce tun a baya ya fahimci cewa ya amince ya auri na miji, a inda ya kara da cewa bai taba jin kunya da ya tsinci kansa a luwadi ba.