Ivory Coast za ta zauna a Sao Paulo

Ivory coast mascot
Image caption Kasar na sa ran taka rawar gani a Brazil 2014

Kocin Ivory Coast, Sabri Lamouchi, ya ce 'yan wasan kasar za su zauna a Sao Paulo a lokacin gasar cin kofin duniya a watan Yuni da Yulin bana a Brazil.

Kasar ta zabi ta zauna a Otal din Oscar Inn Eco Resort.

Lamouchi ya kara da cewa za su fara ya da zango a Porugal domin karawa a wasannin sada zumunci guda biyu, kafin su isa kasar Brazil.

Kocin ya ce, "yana da kyau mu shiga gasar kofin duniya a Brazil da karfin gwiwa, domin kammala gasar da za muyi alfahari da kyakkyawan sakamako''.

Ivory Coast tana rukuni na uku tare da Japan da Colombia da Greece.