Johnson ya bar FA don kyamar luwadi

Image caption Michael Johnson ya ce ba zai iya kare luwadi ba saboda ya saba wa addini.

Michael Johnson ya sauka daga mukaminsa na majalisar shawara kan bai wa kowa dama a harkar kwallon kafa a Ingila bayan da ya bayyana luwadi a matsayin abin kyama.

Michael Johnson tsohon dan wasan Notts County, Birmingham City da Derby County ya bayyana haka ne a 2012 amma sai makon jiya zancen ya tashi.

A wani shiri na BBC ne aka tambayi tsohon dan wasan na Jamaica ko zai goyi bayan gangamin da hukumar kwallon kafa ta FA ke yi na kare 'yancin masu luwadi kasancewarsa mabiyin addinin Kirista.

Ya ce; "Saboda imanin da na yi da littafin Baibul din da nake karanta wa na tabbatar luwadi da madigo abin kyama ne ga Ubangiji."