Mikel na son zama gwarzon Afirka

John Mikel Obi
Image caption Dan wasan ya taka rawar gani a kakar wasan bara

Dan wasan Nigeria John Mikel Obi na fatan lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na shekara ta 2013 da za a sanar da zakara a ranar Alhamis.

Dan kwallon Chelsea mai wasan tsakiya yana takara tare da Yaya Toure mai wasa a Manchester City da kuma Didier Drogba dake buga kwallo a Galatasaray ta Turkiya.

Mikel dan wasan da ya lashe kyautar matashin dan kwallon Afirka karo biyu, ya ce "abun alfahari ne da nake cikin 'yan takara, ina fatan zan lashe kyautar saboda kasa ta."

Dan wasan mai shekaru 26 ya taimakawa Najeriya lashe kofin Nahiyar Afirka karo na uku a watan Fabrairu, da kuma samun gurbin shiga kofin duniya karo biyar da Nigeriya ta yi.

Haka kuma ya Lashe kofin gasar Turai wato UEFA Europa League a Chelsea.

'Yan wasan Najeriya da suka lashe kyautar sun hada da Rashidi Yekini da Emmanuel Amuneke da Victor Ikpeba, kuma Nwankwo Kanu ne dan wasan Nijeriya na karshe da ya lashe kyautar a shekarar 1999.