Rafari ke cutar mu - Moyes

Image caption Karo na farko tun 2001 da United ta fadi wasa uku a jere.

David Moyes ya ce rafari ne ke cutar Manchester United bayan da ta sha kaye 2-1 a hannun Sunderland a karo na farko na matakin kusa da na karshe na gasar kofin Capital One.

Kocin na United ya fusata ne da fenaritin da aka bai wa Adam Johnson wacce ta yi sanadiyyar kwallon da Fabio Borini ya zura, abinda ya bai wa Sunderland nasara a wasan.

A farkon watan nan Moyes ya ce rashin bai wa Manchester United fenariti daf da tashi wasan da Tottenham ta doke a Old Trafford a gasar Premier "abin kunya" ne.

Kayen da kungiyar ta sha ranar Talata na nufin ta yi asarar wasanni uku a jere ke nan a karo na farko tun 2001, kasancewar Swansea ta kore ta daga gasar kofin kalubale ranar Asabar bayan kayen 2-1 da Spurs din ta yi ma ta.