FA ta ci tarar Rodgers fan 8,000

Brendan Rodgers
Image caption Kocin tun farko ya amince da tuhumar da FA ta yi masa

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar kocin Liverpool Brendan Rodgers fan 8, 000, bisa kalaman da ya yi bayan da Manchester City ta doke su a wasan Premier.

Rodgers, wanda ya amince da tuhumar da hukumar tayi masa ranar Laraba, an kuma gargade shi da ya kaucewa farurar hakan nan gaba.

Kocin ya soki korewar alkalin wasan Bolton Lee Mason da neman ba'a sin yadda aka bashi damar alkalancin karawar da suka yi da City.

Kocin Liverpool daga baya ya wanke kansa a kalaman da ya yi ranar 26 ga watan Disamba da cewar bai zargi kwarewar alkalin wasan ba.