Man City ta ragargaji West Ham 6-0

Image caption Allardyce ya ce Manchester City ba sa'ar West Ham ba ce

Magoya bayan West Ham United sun nuna fushinsu ga koci Sam Allardyce bayan da su ka sha lalas sau biyu cikin mako guda - wannan karon a hannun Manchester City.

Mutane biyun da su ka mallaki kungiyar sun bayyana goyon bayansu ga kocin bayan ragargazar 5-0 da kungiyar ta sha a karonta da Nottingham Forest mai buga wasa a rukunin Championship a gasar cin kofin kalubale.

Sai dai magoya bayan kungiyar sun ce ba da su ba, bayan da Manchester City ta yi musu luguden kwallaye 6-0 a zagayen farko na matakin kusa da na karshe a gasar kofin Capital One.

Alvaro Negredo ya ci kwallaye uku a wasan da ya mayar da jimillar kwallayen da Manchester City ta ci a wasanni 15 a gida ta kai 59, yayin da magoya bayan West Ham da ruwa ya jika sharkaf suka bige da wakokin tur da kocinsu.

Sai dai Sam Allardyce wanda ya ce zai ci gaba da rike matsayinsa na kocin West Ham ya ce ai dama Manchester City ba sa'anninsu ba ne.