Messi ya dawo da karfinsa

Image caption Gwarzon dan kwallon duniya, Lionel Messi

Lionel Messi ya zura kwallaye biyu a wasansa na farko bayan murmurewa daga rauni, a wasan da Barcelona ta casa Getafe daci hudu da nema a gasar Copa del Rey.

Dan kwallon Argentina din ya shiga wasan a minti na 63 inda ya maye gurbin Andres Iniesta kuma yaci kwallaye biyu a yayinda Cesc Fabregas shima yaci biyu.

Tun a ranar 10 ga watan Nuwamba rabon da Messi ya buga kwallo saboda rauni.

Dawowarsa za ta karawa Barcelona kwarin gwiwa a yayinda za ta kara da Atletico Madrid a ranar Asabar a gasar La Liga.

Karin bayani