Moyes na jerin kocin da za a zaba a Disamba

David Moyes
Image caption Kocin ya samu koma baya tun komawarsa United

Kocin Manchester United, David Moyes, yana cikin jerin kociyoyin da za a zaba don bai wa kyautar gwarzon kocin gasar Premier na watan Disamba.

United ta yi rashin nasara a wasanni uku a jere, amma ta lashe wasanni hudu da kunnen-doki a wasa daya da kuma rashin nasara a wasanni biyu daga cikin wasanni bakwai da ta kara a gasa daban-daban a watan jiya.

Shi ma kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, da ya lashe dukkan wasanninsa na watan jiya, yana daga cikin jerin kociyoyin da ake sa ran zaba a gwarzon watan jiyan.

Sauran jerin kociyoyin sun hada da Jose Mourinho na Chelsea da kocin Everton Roberto Martinez.

'Yan wasa shida ne suke cikin jerin fitaccen dan kwallon da za a zaba wanda ya fi fice a watan jiya, ciki har da Luis Suarez na Liverpool da ya zura kwallaye 20 a wasanni 15 da ya bugawa Liverpool.

Sauran 'yan wasa sun hada da 'yan kwallon Manchester City Alvaro Negredo da Vincent Kompany da Yaya Toure.

Shi ma dan wasan Everton Ross Barkley da kuma dan kwallon Arsenal Theo Walcott, wanda ya ji raunin da zai yi jinyar watanni shida yana cikinsu.