Yaya Toure ne zakaran kwallon Afrika 2013

Yaya Toure
Image caption Ya zama gwarzon dan kwallon Afirka karo uku a jere

Dan wasan kasar Ivory Coast da Manchester City Yaya Toure ya lashe kyautar zakaran Dan Kwallon Afirkan CAF a karo na uku a jere.

Mikel Obi dan wasan Nijeriya mai buga kwallo a Chelsea ne na biyu a gasar zakaran kwallon Afirka wadda CAF ke shiryawa.

Yayin da Didier Drogba na Ivory Coast dake wasa a Galatasaray dake Turkiya ya yi na uku.

Toure, mai shekaru 30, ya lashe kyautar ne da kociyoyin kasashe ko diractan tsare-tsare na mambobin hukumar CAF da ke yi, a bikin da aka gudanar a Legas dake Nijeriya.

Sauran kyaututtukan da aka lashe sun hada da kyautar gwarzon dan kwallon Afirka dake taka leda a gida, wanda Mohamed Aboutrika ya lashe a karo na hudu, ya taba dauka a shekarun 2006 da 2008 da 2012 da kuma kyautar bara.

Dan kwallon Nijeriya Kelechi Iheanacho shine ya karbi kyautar matashin dan kwallon Afirka mai taso wa, Stephen Keshi ya lashe kyautar kocin Africa da yafi fice, kuma Super Eagles ce ta karbi kyautar kungiyar kwallon Afirka da babu kamarta a bara.