'Watakila Toure ya zama gwarzon Afrika'

Yaya Toure
Image caption Zakaran gwarzon Afirka mai kambu biyu a jere

Ana sa ran dan kwallon Manchester City, Yaya Toure, dan Ivory Coast ne zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na bara da za a sanar da zakara a ranar Alhamis.

Idan ya lashe kyautar zai zama zakaran Afirka karo na uku a jere --- ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na BBC a watan Disamba.

Dan wasan yana takara ne tare da dan kwallon Ivory Coast Didier Drogba da ke wasa a Galatasaray ta Turkiya da dan kwallon Nijeriya mai wasa a Chelsea John Obi Mikel.

Za a gudanar da bikin zaben gwarzon dan kwallon Afirkan bana ne a birnin Legas da ke Nijeriya.

Toure, mai shekaru 30, bai samu lashe kofuna ba a kungiyarsa da kasar saba, amma kwazon da ya nuna a bara ya kara haskaka dan wasan a kungiyarsa da kasarsa Ivory Coast.