Har yanzu Masu West Ham na goyon bayan Allardyce

Sam Allardyce
Image caption Kocin ya gamu da koma baya a gasar kakar wasan bana

Har yanzu Mutane biyun da suka mallaki kungiyar West Ham, David Gold da David Sullivan na goyon bayan koci Sam Allardyce duk da casa su 6-0 da aka yi.

Kungiyar ta sha kashi a hannun Manchester City ne a wasan kusa da na karshe na gasar League Cup.

Kafin wannan wasan West Ham ta sha kayen 5-0 a hannun Nottingham Forest mai buga wasa a rukunin Championship a gasar cin kofin kalubale ranar Lahadi.

West Ham dai ita ce ta biyun karshe a teburin Premier bayan da ta samu nasara daya tal cikin wasanni 13.

Allardyce, mai shekaru 59, ya ce zai ci gaba da kokarin kar su fado daga gasar Premier, za kuma su saka kaimi a karawar da za suyi da Cardiff City ranar Asabar.