Nigeria za ta sada zumunci da Mexico

Image caption Nigeria ce ta lashe gasar kofin Afrika a 2013

Nigeria za ta kara da Mexico a wasan sada zumunci a ranar 5 ga watan Maris a shirye-shiryenta na tunkarar gasar cin kofin duniya.

Za su fafata ne a filin wasa na Georgia Dome dake Atlanta a Amurka.

Wasan na daga cikin karawar da Najeriyar ta tsara don shiryawa gasar da za a buga a Brazil.

Nigeria na rukuni daya tare da Argentina da Iran da kuma Bosnia-Herzegovina a gasar da za a soma a watan Yuni.

Gasar Brazil ta 2014 ita ce gasar cin kofin duniya a karo na biyar da Nigeria za ta hallata.