Ina fatan za mu kara kaimi — Moyes

David Moyes
Image caption Kocin na fatan 'yan wasa za su kara kaimi

Kocin Manchester United David Moyes ya ce yana fatan kungiyarsa za ta kara kaimi a wasanninta bayanda suka doke Swansea da ci 2-0, nasarar data kawo karshen rashin lashe wasanni uku a jere a shekarar 2014.

'Yan wasan United Antonio Valencia da Danny Welbeck ne dai suka zura kwallaye a ragar Swansea, kuma ya rage tazarar maki hudu tsakaninta da Everton dake matsayi na hudu a teburin Premier.

Moyes ya ce "Ina fatan za mu dawo kan ganiyarmu, kuma hakan zai rage mana matsi da muke fuskanta."

Nasarar da United ta samu ta zo ne a lokacin da kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Swansea har gida a kofin FA da kuma duka da tasha a hannun Sunderland a wasan Capital One Cup wasan farko na kusa da na karshe.

Moyes, mai shekaru 50, hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tararsa a bisa caccakar alkalin wasa da ya yi a filin Stadium of Light.