An sallami Guy Demel daga asibiti

Guy Demel
Image caption West Ham na fama da 'yan baya masu jinya a bana

An sallami dan kwallon West Ham mai tsaron baya Guy Demel daga asibiti bayan da ya ji rauni a kansa, lokacin da suka doke Cardiff da ci 2-0 har gida a ranar Asabar.

Demel, mai shekaru 32, sai da aka saka masa abin numfashi a lokacin da aka dauke shi daga filin wasa a sume, a karon da suka yi da dan kwallon City Fraizer Campbell.

Dan kwallon Ivory Coast ya gamu da buguwa a kansa da ya dauki lokuta kafin ya farfado daga suman da ya yi.

West Ham ta hadu da koma baya a wasan, a inda dan wasanta na baya James Tomkins aka bashi jan kati.

Tomkin, ya dawo bugawa kungiyarsa wasa ne bayan da bai samu damar buga wasanni uku baya ba, sakamakon jinya rauni da ya yi.

Haka koci Sam Allardyce ya yi rashin 'yan wasan baya biyu da suka hada da Winston Reid da James Collins da suke jinya.

Kafin West Ham ta lashe wasan jiya, an dura mata kwallaye 11 a raga a wasanni biyu data kara a kofin FA da Leageu Cup.