Ronaldo ake hasashen lashe Ballon d'Or

Cristiano Ronaldo
Image caption Da yammaci za a bayyana gwarzon dan kwallon duniya

Dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ne ake hasasshen zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na bara wato Fifa Ballon d'Or da za a bayyana ranar Litinin.

Kaftin din Portugal mai shekaru 28, na takara ne tare da dan kwallon Barcelona Lionel Messi da Franck Ribery dake wasa a Bayern Munich ta Jamus.

'Yan wasan uku dai an zabo su ne daga cikin 'yan kwallo 23, da za a sanar da gwarzon bara a bikin da Fifa za ta gabatar a Zurich.

Sauran kyaututtuka bakwai da ake sa ran lashewa sun hada da kungiyar 'yan kwallon Fifa su 11.

Haka kuma 'yan wasa uku ne ke takarar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta duniya da suka hada da Nadine Angerer ta Jamus da Marta ta Brazil da Abby Wambach ta Amurka.

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson na cikin takarar kocin da yafi fice a bara, tare da tsohon kocin Bayern Munich Jupp Heynckes da Jurgen Klopp kocin Borussia Dortmund.

Kyautar Kocin da tafi fice a bara kuwa sun hada da kocin Wolfsburg Ralf Kellermann da Silvia Neid mai horar da Jamus da kuma koci Pia Sundhage mai horar da Sweden.