Nasri zai yi jinyar makwanni takwas

Samir Nasri
Image caption An za ci dan kwallon zai yi jinya mai tsawo

Dan kwallon Manchester City mai wasan tsakiya Samir Nasri zai yi jinyar makwanni takwas, bayan da ya samu buguwa a gwiwarsa a wasan da suka doke Newcastle a ranar Lahadi.

Nasri, sai fitar da shi aka yi daga fili, bayan da Mapou Yanga-Mbiwa ya yi tokareshi a gwiwa lokacin wasan.

Tun farko an zaci dan kwallon zai yi jinya mai tsawon gaske da zai dade bai dawo buga kwallo ba.

Dan wasan Faransa ya ji raunin ne a minti na 79 aka saka James Milner ya sauya shi, lokacin da likitoci su ka duba lafiyarsa a cikin fili kafin a daure masa kafa aka fitar da shi.