Ballon d'Or: Ronaldo ya doke Messi

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya lashe kyautar karo na biyu kenan

Dan wasan Portugal da Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya lashe gasar gwarzon kwallon duniya ta ballon d'Or ta 2013.

Kyaftin din na Portugal mai shekaru 28 ya doke Lionel Messi ne na Argentina da Barcelona da Frank Ribery na Faransa da Bayern Munich.

Ronaldo ya zura kwallaye 66 a raga cikin wasanni 56 da ya buga wa kasarsa da kungiyarsa.

Wannan ne karo na biyu da Ronaldo ya samu kyautar bayan da ya taba lashe ta a 2008.

Mai tsaron ragar Jamus ce Nadine Angerer ta lashe kyautar 'yar wasan da tafi fice a bara, sai tsohon kocin Bayern Munich Jupp Heynckes ya lashe kyautar gwarzon koci.

Ronaldo ya lashe kyautar ne da maki 1,365 sai Messi a matsayi na biyu da maki 1,205 Ribery na uku da maki 1,127 a cikin kuri'u 184 da kociyoyi suka yi zabe da kaftin kasashe su 184 da kuma wasu fitatun 'yan jaridun duniya da suka yi zaben.