Fulham na zawarcin Morrison

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ravel Morrison ya ci kwallo 5 a wasa 20.

Kocin Fulham Rene Meulensteen ya ce West Ham ta ki karbar tayin dan wasanta Ravel Morrison da kungiyar ta yi.

Meulensteen ya san tsohon dan wasan na Manchester United mai shekaru 20 daga lokacin da yake cikin masu horar da kungiyar.

Ya ce ya na da tabbacin Morrison na son koma wa Fulham duk da yake West Ham ta raina tayin da aka yi masa.

Meulensteen ya ce za'a iya daidaita wa tsakanin kungiyoyin biyu kafin rufe kasuwar 'yan wasa a karshen watan Janairu.