Pellegrini ya jinjina wa Aguero

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aguero ya zura kwallo a wasansa na farko bayan dawowa daga jinya.

Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini ya jaddada muhimmancin Sergio Aguero bayan da dan wasan ya zura kwallo a ragargazar da kungiyar ta yi wa Blackburn a gasar kofin kalubale, wasansa na farko bayan dawowa daga jinya.

Tun 14 ga Disamba dan Argentinan mai shekaru 25 ya tafi jinyar, amma ya zura kwallo a wasansa na farko da City ta lallasa Blackburn 5-0, abinda ya kai ta mataki na hudu inda zata kara da Watford.

Pellegrini ya ce: "Dawowar Sergio tare da cin kwallonsa abu ne mai muhimmanci saboda muna da wasanni da dama a gabanmu."

City dai na fuskantar wani siratsi a cikin makonni uku masu zuwa a gasar Premier, kofin kalubale da Capital One a yayin da Pellegrini ke neman lashe kofi hudu a kakar wasansa ta farko a Ingila.

Karin bayani