Ronaldo ya zura kwallo bayan lashe Ballon d'Or

cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwarzon Ballon d' Or da Fifa ta zaba na bara

Cristiano Ronaldo ya yi bikin lashe gwarzon dan kwallon duniya bayan da ya zura kwallo a karawar da Real Madrid ta doke Osasuna da ci 2-0 a wasan kofin Copa del Rey.

Dan wasan mai shekaru 28, ya lashe gwarzon dan kwallon duniya ranar Litinin, ya yi murna a kwallon da ya zura a bugun tazara.

Angel di Maria ne ya kara kwallo ta biyu kafin daga baya Gareth Bale ya maye gurbin Ronaldo a minti na 68 da fara kwallo.

Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye 37 a wasanni 28 da ya buga wa kungiyarsa da kasarsa a kakar wasa ta bana.

Real za ta kara da Espanyol wacce ta doke Alcorcon da ci 4-2 a wasan daf da na kusa da karshe,

Athletic Bilbao za ta karbi bakuncin mai rike da kambun bara Atletico Madrid, yayinda Barcelona da Levante za su fafata, bayan da Barca ta doke Getafe da ci 4-0 a wasanni biyu jumulla ranar Alhamis.