Anderson ya koma Fiorentina

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Oliviera Anderson baya samun damar taka leda karkashin Moyes

Dan kwallon Manchester United Anderson na gab da koma wa Fiorentina a inda ake gwada lafiyarsa kafin ya kulla yarjejeniya da ita.

Dan Brazil din ya buga wa United wasanni 177 tun da ya koma kungiyar daga FC Porto a shekara ta 2007.

Wasanni uku kawai aka soma dashi tunda David Moyes ya maye gurbin Sir Alex Ferguson a matsayin kocin United.

Anderson ya koma United ne a kan wata yarjejeniya ta fan miliyan 30 da aka yi musu kudin goro tare da Nani.

Fiorentina a halin yanzu ita ce ta hudu a kan teburin gasar Serie A ta Italiya a yayinda Juventus ke kan gaba.

Karin bayani