Bertrand ya koma Aston Villa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan kwallon Chelsea Ryan Bertrand

Aston Villa ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Chelsea Ryan Bertrand a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan Ingila mai shekaru 24, sau uku kawai aka soma wasa dashi a kakar wasa ta bana karkashin Jose Mourinho a Chelsea.

Bertrand ya buga wasansa na farko a gasar Turai, a wasan da Chelsea ta doke Bayern Munich a gasar zakarun Turai a shekara ta 2012.

Kocin Villa Paul Lambert ya ce "Ryan zai kawo mana kwarewarsa a cikin tawagarmu".

Bertrand wanda ya soma bugawa Chelsea a watan Afrilun 2011, ya taba tafiya aro a kungiyoyin Bournemouth, Oldham Athletic, Norwich City, Reading da kuma Nottingham Forest.

Karin bayani