Dan Nigeria Echiejile ya koma Monaco

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan Nigeria Elderson Echiejile

Dan kwallon Nigeria Elderson Echiejile ya koma kungiyar Monaco ta Faransa daga Sporting Braga ta Portugal.

Dan shekaru 25, Echiejile ya buga wa Nigeria duka wasanninta a lokacin gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a shekara ta 2013.

A yanzu haka dai Monaco ce ta biyu a kan teburin gasar kwallon Faransa, inda Paris St-Germain ke sama.

Kungiyar tana kashe kudi wajen sayen 'yan kwallo, inda a baya ta sayi Radamal Falcao da Joao Moutinho da kuma Lacina Traore.

'Yan Nigeria da dama sun bugawa Monaco a shekarun baya ciki hadda Victor Ikpeba, Lukman Haruna, Sani Keita da kuma Rabiu Afolabi.