FA ta ci tarar Moyes fan dubu takwas

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Moyes

Hukumar kwallon Ingila -FA ta ci tarar kocin Manchester United David Moyes fan dubu takwas sannan ta gargade shi ya san irin yadda zai dunga magana.

An ci tararsa sakamakon kalamansa bayan da United ta sha kashi a wajen Sunderland da ci 2 da 1 a gasar kofin Capital One.

Moyes dan shekaru 50 ya ce " zai soma dariya game da hukuncin da alkalan wasa ke dauka".

Kocin ya amince da saba ka'ida game da dokokin hukumar kwallon Ingila.

A makwannin da su ka wuce aka ci tarar kocin Liverpool, Brendan Rodgers fan dubu takwas a kan kalaman da ya yi wa alkalin wasa Lee Mason, bayan sun sha kashi a wajen Manchester City.

Karin bayani