Neymar zai jinyar wata guda

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Neymar

Dan kwallon Barcelona Neymar zai yi jinyar akalla wata guda saboda rauni a idon sawunsa na dama.

Dan Brazil din mai shekaru 21 ya ji rauni a wasansu da Gatafe na gasar kofin Copa del Rey.

Neymar ya koma Barcelona daga Santos a kan fan miliyan 50 a farkon kakar wasa ta bana, kuma wannan raunin zai hana shi buga wasansa da Levante, Malaga da kuma Valencia.

A yanzu haka dai Barcelona ce a saman teburin gasar La Liga inda take gaban Atletico Madrid da kuma Real Madrid.

Karin bayani