Pochettino zai zauna a Southampton

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mauricio Pochettino

Manajan Southampton Mauricio Pochettino zai bayyana makomarsa a karshen kakar wasa ta bana.

Pochettino ya ba da tabbacin ci gaba da zama a kungiyar bayan da shugabanta Nicola Cortese ya barta.

Saura watanni 17 kwangilarsa ta kware kuma ya ce babu dalilin da zai sa ya bar kungiyar a tsakiyar kakar.

Ya shaidawa BBC cewa: "Bayan kammalawa, zamu duba lamarin mu kuma bayyana ko zamu ci gaba da zama a kungiyar."